‘Yan Gudun Hijira Sama da 100,000 aka mayar Muhallinsu daga Gabar tafkin Chadi

Rundunar  sojin Najeriya, ta ce sama da ‘yan gudun hijira 100,000 ne aka mayar da su gidajen su da ke yankin tafkin Chadi a wani bangare na nasarorin da aka samu kan ‘yan ta’adda a yankunan da ke kan iyakokin Najeriya, wato Nijar da Chadi da Kamaru.

Kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF), Manjo Janar Abdul Khalifah Ibrahim, shine ya bayyana hakan a barikin sojoji na Maimalari, da ke birnin Maiduguri yayin bikin mika lambar yabo ga jami’ai da sojoji da suka shiga aikin Operation Lake Sanity da aka kammala.

Ibrahim ya bayyana cewa an dawo da harkokin tattalin gudanarwa da zamantakewa a cikin al’umma da ke kauyukan da suka koma.

Ya ce, “Abubuwa suna sauki, muna samun raguwar hare-hare a wadannan yankuna, idan kuma aka samu raguwar hare-haren za a samu raguwar illolin da abin ke haifarwa. An samu raguwar hare-haren da ake kaiwa fararen hula sannan kuma an samu raguwar hare-haren hatta a wuraren da sojojinmu suke aiki kuma hakan na faruwa ne sakamakon karuwar hare-haren da sojoji ke kaiwa masu dauke da makamai.

“A cikin shekara guda da ta wuce a cikin yankunan tafkin Chadi, sama da mutane 100,000 ne suka koma gidajesu, mutanen da ko dai ‘yan gudun hijira ne a wasu kasashe ko kuma wadanda suka kasance na cikin giuda ne. Sun dawo wurare kamar su Banki, Cross Power, Baga, duk a cikin Najeriya suke. Idan ka je Nijar kamar Baroua, idan ka je Chadi kamar Bitiri da Kamaru kamar Amchibi da Gulafata mutanen sun koma kauyukansu,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.