Tsohon Shugaban Tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev ya mutu yana da shekaru 91

Shugaban Tarayyar Soviet na karshe Mikhail Gorbachev, ya mutu yana da shekara 91.

Mista Gorbachev, wanda ya karbi ragamar mulki a 1985, ya yi fice wajen bude kofofin tsohuwar Tarrayar Soviet da kuma kusancinsa da kasashen Yamma, amma ya kasa hana kasarsa rugujewa a 1991.

ana ganin rushewar ta rayyar sovirt na da alaka da tsare-tsaren sa  na kawo sauyi a lokacin da yake jagorantar tarayyar ta soviet .

Jami’an asibitin da ya mutu sun ce ya yi fama da doguwar rashin lafiya.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana alhininsa game da mutuwar Mista Gorbachev, kamar yadda mai magana da yawunsa Dmitry Peskov ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Rasha Interfax a cewar Reuters.

Mista Gorbachev ya zama babban sakataren jam’iyyar gurguzu ta tsohuwar Tarayyar Soviet da kuma shugaban kasa yana da shekara 54.

A wancan lokaci shi ne mamba mafi karancin shekaru a majalisar da ke mulki da aka fi sani da Politburo, kuma ana kallonsa a matsayin matashi mai kwarjini, bayan shekarun da aka shafe ana samun shugabannin da suka tsufa.

Manufarsa ta bai wa al’ummar kasar damar bayyana ra’ayoyinsu ciki har da sukar gwamnati wanda wani abu ne mai wuya a baya.

Sai dai ta sa yankuna da dama sun fara neman ‘yancin kai, wanda a karshe ya kai ga rugujewarta.

A matakin kasa da kasa ya cimma yarjejeniyar takaita amfani da makamai tsakanin kasarsa da Amurka, kuma ya ki shiga tsakani a lokacin da kasashen gabashin Turai suka yi wa shugabanninsu masu ra’ayin gurguzu bore.

Kasashen yammacin duniya na kallonsa a matsayin wanda ya jagoranci yadda za a kawo karshen yakin cacar-baka.

An ba shi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a shekara ta 1990, saboda rawar da ya taka wajen kawo sauye-sauye a dangantakar da ke tsakanin kasashen Gabashi da na Yamma.

Leave a Reply

Your email address will not be published.