Tsohon shugaban kwastam na Najeriya, Hamman Ahmad, YA RASU.

Tsohon shugaban hukumar hana fasakwauri na kasa, kwastam, Hamman Ahmad, ya riga mu gidan gaskiya, Ya rasu ne a ranar Laraba yana da shekaru 78 a duniya.

Mr Ahmad ya rasu ne yayin da ake masa magani a wani asibiti a Abuja. Rasuwarsa na zuwa ne bayan wani tsohon shugaban na kwastam, Dikko Inde, ya rasu a watan Fabrairu da ta gabata. Marigayi Ahmad dan asalin karamar hukumar Jada ne da ke jihar Adamawa kuma za a yi jana’izar sa ne a ranar Laraba a masallacin kasa da ke Abuja.

Mr Ahmad ya rike kujerar shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya ne daga shekarar 2008 zuwa 2009 a lokacin mulkin Shugaban Kasa Umaru Musa Yar’Adua. Shi ne ya gaji kujerar daga hannun Bernard Nwadialo kuma Jacob Buba ya gaje shi. Kafin ya rike mukamin shugaban hukumar, shi ne mataimakin shugaban hukumar a hedkwatar ta da ke Abuja. Marigayin ya yi karatun sa na firamare a makarantar firamare ta Jada daga shekarar 1956 zuwa 1963 daga nan ya zarce Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Ganye inda ya yi karatu daga 1965 zuwa 1969.

Ya samu takardar shedar WAESC a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Bauchi a shekarar 1970 sannan ya zarce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a 1977 inda ya yi digirinsa na farko. Bayan ya yi hidimar kasar sa shekarar 1978 ya fara aiki da Hukumar Kwastam ta Kasa a matsayin Assistant Superintendent. Ya yi ayyuka a rassan hukumar na daban-daban kamar; Valuation Unit, Hedkwatar Kwastam da kuma Tin Can Island inda daga nan ya samu karin girma ya zama mataimakin shugaban hukumar a 2005, sannan ya rike kujerar Jami’in sa ido a hedkwatar kwastam din har watan Mayun 2008 bayan nan ya zama shugaban hukumar.

Ahmad ya rasu ya bar matan sa biyu da yara, jikoki da kuma kannin sa maza.

Cikin ‘yan uwansa akwai Usman Ahmad (Shehu Kojoli) wanda ya yi murabus daga shugaban Hukumar Gidajen Gyaran Hali da Umar Ardo dan takarar gwamnan Jihar Adamawa kuma tsohon mai bai wa Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo shawarwari kan harkokin kananan hukumomi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.