Sojin Najeriya sun sami nasarar kama ‘yan ta’adda 79 a yankin arewa maso gabashin kasar

Dakarun Najeriya karkashin runduna ta musamman ta ‘Operation Hadin Kai’’, sun cafke ‘yan ta’adda akalla 79 tare da masu taimaka musu a yankin Arewa maso gabas cikin makwanni biyu da suka gabata.

Darakta mai kula da harkokin yada labarai na ma’aikatar tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami, ne ya bayyana hakan jiya Alhamis a Abuja, yayin taron manema labarai na mako biyu kan ayyukan rundunar.

Manjo Janar Danmadami ya kara da cewar sojojin Najeriyar sun kashe ‘yan ta’adda da dama, yayin farmakin da suka kaddamar akansu ta sama da kasa, tare da kubutar da mutane 14 da suka yi garkuwa da su, ciki har da ‘yan matan sakandiren  Chibok biyu a tsawon makwanni biyun.

Danmadami ya bayyana sunan ‘yan matan da aka ceto da Yana Pogu da kuma Rejoice Senki tare da ‘ya’yansu da suka Haifa da mayakan na Boko haram wadanda suka sace su tun shekarar 2014.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *