Shekara daya da cikar Taliban kan mulkin Kasar Afghanistan

Taliban ta aiyana wannan Litinin a matsayin ranar hutu don murnar ranar da ta yi nasarar karbe iko tare da tilasta wa rundunar Amirka ficewa daga cikin kasar, bayan shafe kusan shekaru ashirin da Amirkan ta yi da sunan son samar da zaman lafiya a kasar.

Sai dai rahotanni na kungiyoyi masu aikin agaji a kasar, sun nuna yadda Afghanistan ta sake tsintar kai a cikin tsanani na talauci da kuma zarge-zarge na tauye hakki da cin zarafin mata da ‘yan mata da hanasu neman ilimi. A rana mai kamar ta yau, sha biyar ga watan Agustan bara, Taliban ta hambarar da gwamnatin Ashraf Ghani, wanda daga bisani ya tsere daga kasar ya kuma nemi mafaka a Dubai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.