Sakataren Harkokin Amurka Antony Blinken Ya isa kasar Rwanda

Ziyarar ta Mr blinken na zuwa daidai lokacin da ake dakonta inda ake saran tattauna kan zarginda akewa kasar ta Ruwanda kan tallafa wa ‘yan tawayen M23 dake ayyukansu akasar kwango 

 

Anasaran Mr bliken zaiyi amfani da damar amurica wajen matsawa mahukuntan birnin Kigali domin sakin Poul Rusesabagina mutumin da yasamu lambar Oscar kan harkokin finafinai wanda Kuma Amurica ta bayyana cewar bisa kuskurene aka kamashi

An dai yankewa Rusessagina hukuncin daurin shekaru 25 ne a gidan yari bisa zargin  ayyukan ta addanci a shekarar da ta gabata

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana Cewar Mr,Bliken zai kuma gana da Shugaban Kasar Rwanda da kuma Kungiyoyin faren hula tareda tattauna muhimman abubuwa akasar

Mr Blinken ya isa Birnin Kigali tun a rananr laraba da daddare kai tsaye  daga birnin Kinshasa a inda mahukuntan kasar suka bukaci da Amurka ta sawa Rwanda takunkumi bisa goyon bayan yantawaye da takeyi na M23a arewacin kasar Demokradiyyar Congo.

inda tuni Rwanda ta musanta zargin.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.