Rundunar Sojan Najeriya tace Anasamun Nasara ayaki da yan Bindiga

Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kashe wani kasurgumin ɗan fashin daji Albdulkarim Boss da mutanansa 27 a karshen mako, bayan barin wutar da wani jirgin yaƙi ya yi a kan maboyarsu.

Abdulkareem Lawal wanda aka fi sani da Abdulkareem Boss, an jima ana farautarsa kafin a hallaka shi a wannan lokaci.

Hare-haren sama da sojojin suka kaddamar na zuwa ne kasa da mako guda da shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da manyan hafsoshin tsaron ƙasar da su ka yi alkawarin kawo ƙarshen matsalolin tsaron Najeriya.

An hallaka ɗan fashin ne a kauyen Marina da ke karamar hukumar Safana ta Katsina.

Abdulkareem ne ya jagoranci muggan hare-haren ta’addanci da dama a yankunan arewacin Najeriya da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Sannan shi ya jagoranci kai hari kan ayarin motocin shugaban kasa a Daura da kuma mutuwar shugaban ‘yan sanda yankin Dustinma a cikin watan Yuli.

An kuma kai irin wadannan hare-haren sama a maboyar ‘yan bindiga a kauyukan Abuja a cewar jaridar PRNigeria.

A cewar rahotanni ‘yan bindiga da ke maboya a dazukan Kaduna da Neja da Zamfara ke haifar da barazanar tsaro a babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published.