Rasha Tabawa kasar Mali Tallafin Jiragen Yaki

Jiragen yaki biyar da kuma mai saukar ungulu guda ne Rasha ta mika wa Mali a wani biki da ya samu halartar shugaban sojin kasar, Assimi Goita tare da jakadun Moscow.

A jawabin da ya yi, Ministan Tsaron Mali, Sadio Camara ya jinjina wa abin da ya kira huldar da kasashen biyu suka ci ribar ta, yana mai cewa, sabbin kayayyakin sojin za su karfafa hare-harensu kan ‘yan ta’adda.

Gwamnatin Mali dai ta gayyato wasu jami’an tsaron sa-kai daga  Rasha, inda ta bayyana su a matsayin masu bada horo, amma kasashen yammaci duniya na kallon su a matsayin sojojin haya daa aka dauko su domin agaza wa dakarun Malin da ke cikin tsaka mai wuya.

Dauko wadannan sojin na Rasha ya taka rawa wajen ficewar Faransa daga kasar ta Mali, ficewar da ake sa ran kammala ta baki daya nan da ‘yan makwanni masu zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.