Odinga zai kalubalanci sakamakon zaben Kenya a kotu

Mako guda bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasar Kenya, Raila Odinga da ya zo na biyu a zaben ya ce zai kalubalanci nasarar da mataimakin shugaban kasar William Ruto ya samu.

A ranar Litinin da ta gabata ne hukumar zaben kasar ta sanar da Ruto a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaben, duk da yake tazarar da ke tsakaninsa da Oginda ba ta wuce kashi biyu ba.

Ba wai bangaren Odinga ne kadai ya ki amincewa da sakamakon zaben ba, domin hudu daga cikin kwamishinonin hukumar zaben  kasar 7 sun ki amincewa da shi.

A Litinin din nan ce dai, shahararren dan siyasar zai gabatar da korafinsa a gaban kotun kolin kasar, inda kuma kotun ke da makwanni biyu don yanke hukunci a kai.

Tun daga shekarar 2002, babu wani zaben shugaban kasa da aka yi a Kenya da ba a kalubalanci sakamakonsa a gaban kotu ba, da kuma zama sanadiyar zubar da jini.

Leave a Reply

Your email address will not be published.