Saturday 3rd of June 2023
No record found
Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28

Majalisar dokokin Najeriya ta yi kira ga babban bankin ?asar da ya tsawaita wa'adin daina amfani da tsoffin takardun ku?in ?asar zuwa wata shida masu zuwa.

Majalisar wakilai da ta dattawan ƙasar sun yi kiran ne a wasu mabambantan zama da suka yi ranar Talata.

Majalisar wakilan ?asar ta ce idan ?asa na bu?atar kowane tsarinta ya kai ga nasara, to dole ta yi la'akari da 'yan ?asa. Majalisar ta ?ara da cewa ta damu matu?a game da yadda wasu 'yan kasuwa ke ?in kar?ar tsoffin takardun ku?in, yayin da bankuna ke ?orafi game da ?arancin sabbin takardun. Majalisar wakilan ta bu?aci shugaban ?asar da ya saka baki game da wannan batu. Dan haka ne ma ta kafa wani kwamiti da zai gana da gwamnan babban bankin da sauran daraktocin bankunan ?asar game da ?orafe-?orafen ?arancin sabbin takardun ku?in. A nata ?angare majalisar dattawan ?asar ta ce ya kamata a tsawaita wa'adin sakamkon yadda har yanzu bankunan ?asar ke saka tsoffin takardun ku?in a na'urorin cirar ku?insu ta ATM. Majalisar dattawan ta kuma koka game da wahalhalun da 'yan ?asar ke fuskanta na bin dogayen layuka a bankuna a fa?in ?asar domin sauya ku?a?ensu.

Ishaq Ahmad
380 2

Ra'ayoyi

Image
Aliyu Diso 2023-01-25 16:51:54

Raayin shi ne kamata yayi shugaban kasa ya karbi wannan kuduri ya aiwatar da shi domin, mutane sun fara galabaita kuma mutane suna asara, ga kuncin rayuwa da hakan ya hefa alumma. Muddin shugaban kasa bai dauki matakin gaggawa ya umarni babban banking kasa ba, baby shakka ya nuna cewa shugaban kasa ba ya damuwa da halin da alummar kasa suka shiga. Sannan kuma zai jawowa jamiyyarsa ta APC asara a zaben 2023 mai zuwa. Wannan mataki bai sace da lokacin da ake neman kuriar mutanen Najeriya ba.

Image
Rayyanu Sani 2023-02-01 09:21:38

ra ayina anan shine agaskiya mutane suna cikin takura sosai idankaje cire kudi abank dogon layi idan katafi POS bakudi ahannusu idanma kasami kudi awajansu chaji yayi yawa idan kaje kasuwa daniyar sayar da kayan noma bakudi ahannun masu saya munakiradababbarmurya atemakawa alumma nageria

Ajiye mana ra'ayinka

Wasikun Labarai

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Muhimmai

Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28
Majalisar dokokin Najeriy
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47
Gwamnatin tarayyar Najeri
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47
Gwamnatin Najeriya na kam
Wasanni / 2023-01-23 13:15:52
MAN UNITED ZA TA KARA DA
Wasanni / 2023-01-23 13:17:01
NAJERIYA TA CI FARANSA, G

Tambarin Hausa

Tambarin Hausa Tv, gidan Talabijin guda daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta da harshen Hausa

Quick Links

© Amasis Broadcasting Services LTD.. All Rights Reserved.