NAJERIYA TA CI FARANSA, GHANA TA SHA KASHI A GASAR KOFIN DUNIYA TA MATA

Najeriya ta doke Faransa 1-0 a wasansu na farko na rukuni na uku, wato Group C, na gasar cin Kofin Duniya na mata ‘yan kasa da shekara 20 a Costa Rica ranar Alhamisjeri. Kwallo daya tilo da Flourish Sabastine ta jefa bayan minti 85 ita ce ta bai wa tawagar ta Falconets maki ukun shan kashi na farko da Faransa ta taba gamuwa da shi a matakin wasannin rukuni na gasar tun da aka kirkiro ta. Tsananin yanayi na iska da ruwan sama a filin wasan na kasa a San Jose, ya sa aka dakatar da wasan tsawon kusan sa’a daya a minti na 21. Wasa na gaba da Najeriyar za ta yi shi ne da Koriya ta Kudu, wadda ta doke Kanada 2-0 a wasansu na farko ranar Lahadi. Daya kasar da ke wakiltar Afirka a gasar wato Ghana ta yi rashin nasara a wasanta na farko a rukuninsu na hudu wato Group D 3-0 a hannun Amurka, bayan da alkalin wasa ya kori Jacqueline Owusu a minti na 31. Amurkar ce dai ta fi kowa ce kasa cin wannan kofi inda ta dauke shi sau uku. A ranar Lahadi ne tawagar ta Ghana, The Black Princesses, wadda ba ta taba wuce matakin wasannin rukuni ba a gasar a zuwanta biyar, za ta fafata da masu rike da kofi Japan. Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashe hudu da ba su taba kuskure zuwa gasar kwallon kafar ta mata ta duniya ‘yan kasa da shekara 20 ba tun da aka kirkiro ta shekara 20 da ta wuce, Sauran kasashen uku su ne Amurka da Jamus da kuma Brazil Idan baamantaba najeriya ta yi nasarar zuwa wasan karshe har sau biyu amma basu iya yin nasar daukar kofin ba in ba;a mantaba a shekara ta 2010 da 2014 sun kai wasan karshen amma basuyi nasaraba

545 123

Ra'ayoyi

Fada mana ra'ayinka

Get In Touch

75 club Road, Kano, Kano State Nigeria

+2349161164442

info@tambarinhausatv.com

Ku bibiyemu
Hotunanmu

© Amasis Broadcasting Services LTD. All Rights Reserved. Design by Smartage softtechs Limited