GWAMNATIN NAJERIYA TA FITAR DA JERIN SUNAYEN ‘YAN TA’ADDA DA TAKE NEMA RUWA A JALLO

Rundunar Tsaron Najeriya ta sanya kyautar Naira miliyan biyar ga duk wanda ya ba da bayani da za su taimaka a kama ’yan ta’adda. A safiyar Litinin rundunar ta fitar da jergin gawurtattun ’yan ta’adda 19 da suka addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, da kuma kyautar da ta sanya a kan kowannensu. Sanarwar da Darektan Yada Labaran Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Jimmy Akpor, ya fitar ta ce yin hakan ya zama dole, domin ta ci gaba da ragargaza da kuma murkushe miyagun gaba daya, domin Najeriya ta samu kwanciyar hankali. Ga yerin sunayen ’yan ta’addan: Sani Dangote: Dan asalin kauyen Dumbarum a Karamar Hukumar Zurmi, Jihar Zamfara Bello Turji Gudda: Dan asalin kauyen Fakaia Jihar Zamfara Leko: Dan asalin kauyen Mozji, Karamar Hukumar Matazu, Jihar Katsina Dogo Nahali: Dan asalin kauyen ’Yar Tsamiyar Ino, Karamar Hukumar Kankara, Jihar Katsina Halilu Sububu: Dan asalin kauyen Sububu, Karamar Hukumar Maradun, Jihar Zamfara Nagona: Dan asalin kauyen Unguwar Galadima, Karamar Hukumar Isa, Jihar Sakkwato Nasanda: Dan asalin kauyen Kwashabawa, Karamar Hukumar Zurmi, Jihar Zamara Isiya Kwashen Garwa: Dan asalin kauyen Kamfanin Duadawa, Karamar Hukumar Faskari, Jihar Katsina. Alia Kachalla (Ali Kawaje): Dan asalin kuayen Kuyambana, Karamar Hukumar Dansadau, Jihar Zamfara Abu Radda: Dan asalin kauyen Zaranda, Karamar Hukumar Batsari, Jihar Katsina Dan-Da: Dan asalin asalin kauyen Zaranda, Karamar Hukumar Batsari, Jihar Katsina. Sani Gurgu: Dan asalin kauyen Zaranda, Karamar Hukumar Batsari, Jihar Katsina Umaru Dan Najeriya: Dan asalin kauyen Rafi a Karamar Hukumar Gusau, Jihar Zamfara. Nagala: Dan asalin Karamar Hukumar Maru, Jihar Zamfara. Alhaji Ado Aliero: Dan asalin kauyen Yankuzo, Karamar Hukumar Tsafe, Jihar Zamfara. Monore: Dan asalin kauyen Yantumaki, Jihar Katsina. Gwaska Dankarami: Dan asalin kauyen Shamushele, Karamar Hukumar Zurmi, Jihar Zamfara. Baleri: Dan asalin Karamar Hukumar Shinkafi, Jihar Zamfera. Mamudu Tainange: Dan asalin kauyen Zaranda, Karamar Hukumar Batsari, Jihar Katsina.

295 123

Ra'ayoyi

Fada mana ra'ayinka

Get In Touch

75 club Road, Kano, Kano State Nigeria

+2349161164442

info@tambarinhausatv.com

Ku bibiyemu
Hotunanmu

© Amasis Broadcasting Services LTD. All Rights Reserved. Design by Smartage softtechs Limited