Saturday 3rd of June 2023
No record found
Tsaro / 2023-01-23 13:13:19

AMURIKA TA GARGADI KAN YUWUWAR KAI HARI HARI A ABUJA

Amurka da Birtaniya a jiya Lahadi sun yi gargadi kan yiwuwar a kai harin ta’addanci a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya, musamman kan gine-ginen gwamnati, wuraren ibada da makarantu, da dai sauransu. Najeriya dai na yakar masu tayar da kayar baya da sunan addini a yankin arewa maso gabas, amma a watan Yuli kungiyar IS ta dauki alhakin wani samame a wani gidan yari da ke Abuja, wanda ya yi nasarar kubutar da fursunoni kusan 440, lamarin da ya haifar da fargabar cewa ‘yan ta’adda masu tayar da kayar baya na kutsowa daga yankunansu. Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce “akwai karuwar kasadar ta’addanci a Najeriya, musamman Abuja” sannan ya kara da cewa manyan kantunan kasuwanci da cibiyoyin tabbatar da doka da kuma kungiyoyin kasa da kasa na daga cikin wuraren da ke fuskantar hadarin. “Ofishin jakadancin Amurka zai yi takaitaccen aiki har sai illa masha Allahu,” in ji ofishin a cikin sanarwar da aka yi wa ‘yan kasar a Najeriya. Gwamnatin Burtaniya ta yi gargadin cewa ‘yan kasarta a Najeriya su kasance cikin shiri saboda “karin barazanar hare-haren ta’addanci a Abuja.” “Harin na iya zama na kan mai uwa da wabi sannan ya na iya rutsawa da muradun Yammacin duniya, da kuma wuraren da ‘yan yawon bude ido kan ziyarta,” a cewarta Rashin tsaro, wanda al’mari ne da ya wansu a Najeriya, zai zama wata babbar matsala yayin da masu kada kuri’a su ka dunguma zuwa runfunan zabe a watan Fabrairu mai zuwa don zaben sabon Shugaban kasa wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari. Ba a samu jin ta bakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeria nan take ba. – Reuters

Ishaq Ahmad
552 0

Ra'ayoyi

Ajiye mana ra'ayinka

Wasikun Labarai

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Muhimmai

Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28
Majalisar dokokin Najeriy
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47
Gwamnatin tarayyar Najeri
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47
Gwamnatin Najeriya na kam
Wasanni / 2023-01-23 13:15:52
MAN UNITED ZA TA KARA DA
Wasanni / 2023-01-23 13:17:01
NAJERIYA TA CI FARANSA, G

Tambarin Hausa

Tambarin Hausa Tv, gidan Talabijin guda daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta da harshen Hausa

Quick Links

© Amasis Broadcasting Services LTD.. All Rights Reserved.