Tsohon Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na kan hanyar samun nasara a babban zaben kasar da aka gudanar, kamar yadda sakamakon ra’ayin wadanda suka kada kuri’a ya nuna. Hasashen ya nuna cewa Mista Natenyahu na kan gaba da ‘yar tazara a yawan kujerun da jam’iyyarsa za ta samu a majalisar dokokin kasar. Wannan sakamako na hasashen dawowar Mista Netanyahu kan karagar mulkin da ya rasa iko da shi ne a shekarar da ta gabata bayan shafe shekara 12 a jere yana jagorantar kasar. Netanyahu ya faɗa wa cincirindon magoya bayansa a birnin Kudus cewa ”muna dab da samun babban nasara”.
Sign up for our news letter and stay up updated
75 club Road, Kano, Kano State Nigeria
+2349161164442
info@tambarinhausatv.com
© Amasis Broadcasting Services LTD. All Rights Reserved. Design by Smartage softtechs Limited