Tuesday 3rd gam October 2023
No record found
Labaran Duniya / 2023-04-01 23:34:46

FADAR SHUGABAN KASA TAYI ALLAH WADAI DA LABARAN KARYA AKAN KIN MIKA MULKI GA GWAMNATI MAI JIRAN GADO

Fadar shugaban kasa tayi Allah wadai da  labaran kanzon kurege  da ke cigaba da karakaiina  a  kafafen yada labarai  a inda ake  yada labaran cewar Shugaba Muhammadu Buhari bazai mika Mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula  ba a inda ya ce  abin takaici ne Kuma abin  Allah wadai .

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce  jaridar  Sahara Reporters na daga cikin wanda suke yada labaran karya domin a cewar sa mamallakin ta dan siyasa ne daga cikin abokan Yan takarar da suka Sha  Kaye a zaben shugaban kasar daya gabata . 

A cewar sa Tuni  gwamnati ta fara shiye shiyen matakin mika mulki.tare da kafa  Kwamitin rikon kwarya wanda ya kunshi wakilan gwamnati mai barin gado da mai jiran gado  wadanda ke yin taro a kusan kullum don tattara bayanan  shirin mika mulki ga gwamnatin Tinubu/Shettima.

Kwamitoci goma sha uku a matsayin na babban kwamitin, wasu da za su shirya atisayen soji da janyewa daga shugaba Buhari, ko dai suna kan aiki ko kuma nan ba da dadewa ba. Ya zuwa yanzu, komai na tafiya yadda ya kamata, kuma babu alamar wata matsala.

Asmau Uba Muhammad
371 0

Ra'ayoyi

Ajiye mana ra'ayinka

Wasikun Labarai

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Muhimmai

Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28
Majalisar dokokin Najeriy
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47
Gwamnatin tarayyar Najeri
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47
Gwamnatin Najeriya na kam
Wasanni / 2023-01-23 13:15:52
MAN UNITED ZA TA KARA DA
Wasanni / 2023-01-23 13:17:01
NAJERIYA TA CI FARANSA, G

Tambarin Hausa

Tambarin Hausa Tv, gidan Talabijin guda daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta da harshen Hausa

Quick Links

© Amasis Broadcasting Services LTD.. All Rights Reserved.