TURKIYYA TA KADDAMAR DA SABON TASHAR WATSA LABARAI NA ZAMANI
Tashar watsa labarai ta Turkiyya ta kaddamar da sabon dandalin labarai na zamani, da akayi wa lakabi da TRT Afrika, don haskaka labaran nahiyar afrika zuwa ga masu sauraro a duniya a cikin harsuna hudu, wanda suaka hadar da harshen Hausa, Swahili, Turanci, da Faransanci.
Tashar ta kaddamar da Shirin ta na farko kai tsaye a ranar Juma a a rana ta biyu na taro na Farko na Watsa Labarai da TRT da Kungiyar Watsa Labarai ta Afirka suka shirya a Istanbul.
An kaddamar da tashar wacce za ta samar da zabi wajen bayar da sahihan labarai game da nahiyar Afirka a birin Istanbul a gaban membobin kungiyar watsa labarai ta Afirka, manyan jami an gwamnati da jami an diflomasiyya.
A jawabin sa Darakta Janar na tashar TRT, Mehmet Zahid Sobaci. Ya bayyana cewa “TRT Afrika za ta kasance dandalin da zai nuna gaskiya da hakikanin gaskiya a Afirka. Shi ya sa takenmu shi ne Afrika, yadda take,”
Ya kara da cewa , al adun Afirka, kyawawan dabi u da kuma labarai masu ma ana na nahiyar ba su ba da isassun labarai daga kafofin watsa labarai na duniya , ya kara da cewa shekaru da dama da suka gabata Afirka ta kasance tana fuskantar manufofin watsa shirye-shirye na zahiri na yammacin duniya.
Har ila yau, tashar za ta ba da murya ga labarai daga Afirka da yan Afirka a cikin kasashen waje, tare da sanya nau in shirye shirye na musamman na ainihin dabi un su a cikin abubuwan da ke faruwa a duniya.
TRT Afirka na da nufin samar da keɓaɓɓen abun a zamance, labarai na musamman, bincike da shirye-shirye na al amuran Afirka na gida ga masu sauraron Afirka da na duniya da kuma biyan buƙatun mazauna Afirka a duk duniya.
Tare da ma aikata daga kasashe 15 na nahiyar, manufar TRT Afrika ita ce ta zama amintaccen majiyar labarai a nahiyar, mai dauke da labaran duniya masu muhimmanci ga masu sauraron Afirka da kuma samar da ingantattun bayanai ga matasa masu alaka da duniya a shafukan sada zumunta.