Tuesday 3rd gam October 2023
No record found
Labaran Duniya / 2023-03-16 14:55:01

An shafe watanni Faransawa na bore akan garambawul ga dokar fansho a kasar.

Majalisar Dokokin Faransa na  shirin kada ƙuri’a don amince wa da yunkurin shugaba Emmanuel Macron na garambawul ga dokar fansho a dai dai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar kalubalantar wannan yunkuri da aka shafe watanni Faransawa na bore akai. 

Tuni dai kwamitocin Majalisar da aka kafa don bibiyar wannan doka suka bayyana amannarsu ga shirin na Emmanuel Macronda zai yi garamabwul ga dokar ritaya ciki har da kara shekarun ritaya daga 62  zuwa  64  duk  da  kakkarfar  zanga-zangar da kasarke gani tunbayan sanar da kudirin. 

Jiya laraba aka cika mako na 8 kungiyoyin kwadago na gudanar da kakkarfar zanga-zanga a sassan Faransar, boren dake gudana hade da yajin aikin sashin sufuri da dukkanin kamfanoni da ma’aikatun makamashi, sai da ialamu na nuna dukkanin wannan bore ya gaza dakile shirin na Macron bayan da Majalisa ke Shirin yi masa zaman karshe a yau alhamis.

Karkashin wannan kudiri na shugaba Macron ya dage alfarmar da wasu daidaikun ‘yan fansho ke samu bayan ritaya. 

Asmau Uba Muhammad
491 0

Ra'ayoyi

Ajiye mana ra'ayinka

Wasikun Labarai

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Muhimmai

Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28
Majalisar dokokin Najeriy
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47
Gwamnatin tarayyar Najeri
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47
Gwamnatin Najeriya na kam
Wasanni / 2023-01-23 13:15:52
MAN UNITED ZA TA KARA DA
Wasanni / 2023-01-23 13:17:01
NAJERIYA TA CI FARANSA, G

Tambarin Hausa

Tambarin Hausa Tv, gidan Talabijin guda daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta da harshen Hausa

Quick Links

© Amasis Broadcasting Services LTD.. All Rights Reserved.