Saturday 3rd of June 2023
No record found
Tsaro / 2023-03-16 14:44:55

Hukumar EFCC za ta jibge jami’anta 200 a jihohin Kano da Katsina da jigawa a lokacin zaben gwamnonin

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC za ta jibge jami’anta 200 a jihohin Kano  da Katsina da jigawa a lokacin zaben gwamnonin da na ‘yan majalisun jihohi da za a gudanar a ranar Asabar

Kwamandan shiyya na jihar Kano Farouk Dogon Daji ya shaida hakan ga manema labarai a Kano a ranar Alhamis.ya na mai cewa za a tura jami’an  zuwa jihohin ne domin sa ido a rumfunan zabe domin hana siyan kuri u yayinda saura za a tura su filayen tashin jiragen saman a Kano da Katsina.

Dogon Daji ya kara da cewa matakin wani yukuri ne na Hukumar EFCC wajen tabbatar da sahihin zabe a shiyyar.

Kwamandan ya kara da cewa Hukumar hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro za su samar da kyakkyawan yanayi domin ganin jama’a sun kada kuri’a cikin lumana da kwanciyar hankali

Asmau Uba Muhammad
342 0

Ra'ayoyi

Ajiye mana ra'ayinka

Wasikun Labarai

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Muhimmai

Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28
Majalisar dokokin Najeriy
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47
Gwamnatin tarayyar Najeri
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47
Gwamnatin Najeriya na kam
Wasanni / 2023-01-23 13:15:52
MAN UNITED ZA TA KARA DA
Wasanni / 2023-01-23 13:17:01
NAJERIYA TA CI FARANSA, G

Tambarin Hausa

Tambarin Hausa Tv, gidan Talabijin guda daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta da harshen Hausa

Quick Links

© Amasis Broadcasting Services LTD.. All Rights Reserved.