TSOHON SHUGABA LULA YA LASHE ZABEN SHUGABAN KASA A BRAZIL

Tsohon shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, inda ya kayar da shugaba mai-ci Jair Bolsonaro wanda ya so samun wa’adi na biyu. Lula ya lashe zaben da kashi 50.83 cikin 100 na dukkan kuri’un da aka kada, yayin da Bolsonaro ya sami kashi 49.17 cikin 100 na kuri’un bayan da aka kidaya kimanin kashi 99 cikin 100 na dukkan kuri’un da aka kada zuwa karfe 11 na dare. Za a rantsar da sabo shugaban kasar ranar 1 ga watan Janairun shekara 2023.

421 123

Ra'ayoyi

Fada mana ra'ayinka

Get In Touch

75 club Road, Kano, Kano State Nigeria

+2349161164442

info@tambarinhausatv.com

Ku bibiyemu
Hotunanmu

© Amasis Broadcasting Services LTD. All Rights Reserved. Design by Smartage softtechs Limited