Saturday 3rd of June 2023
No record found
Kasuwanci / 2023-03-15 21:49:20

An samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a watan Janairun 2023.

Hukumar  Kididdiga ta Najeriya ta ce an samu ƙaruwar hauhawar  farashin kayayyakin  da ya haura zuwa kashi 21.8 cikin ɗari idan aka kwatanta da kashi 21. cikin dari a watan Disamba.

Rahoton ya yi nuni da cewa hauhawar farashin kaya a shekara ya kai kashi 6.2 cikin ɗari idan aka kwatanta da na watan Janairun 2022, wanda ya kai kashi 16.

Rahoton ya ce kayayyakin da farashinsu ya tashi sun haɗa da burodi wanda ya kai kashi 22, da dankali da dawa, da doya da kuma na kayan lambu.

Bugu da ƙari, rahoton ya bayyana cewa farashin kayayyakni a cikin Janairu 2023 ya tashi da kashi 2 a kowane wata.

Haka na zuwa ne yayin da yan ƙasar ke ci gaba da fuskantar matsalar ƙarancin sabbin takardun kuɗi sakamakon sake fasalin kuɗi da gwamnati ta yi.

Matsalar ta jefa ‘yan ƙasar da dama cikin wahalhalu, inda suke fuskantar kalubale wajen biyan bukatun yau da kullum.

Asmau Uba Muhammad
418 0

Ra'ayoyi

Ajiye mana ra'ayinka

Wasikun Labarai

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Muhimmai

Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28
Majalisar dokokin Najeriy
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47
Gwamnatin tarayyar Najeri
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47
Gwamnatin Najeriya na kam
Wasanni / 2023-01-23 13:15:52
MAN UNITED ZA TA KARA DA
Wasanni / 2023-01-23 13:17:01
NAJERIYA TA CI FARANSA, G

Tambarin Hausa

Tambarin Hausa Tv, gidan Talabijin guda daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta da harshen Hausa

Quick Links

© Amasis Broadcasting Services LTD.. All Rights Reserved.