Tuesday 3rd gam October 2023
No record found
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47

Gwamnatin Najeriya na kammala cire tallafin man fetur kafin mika mulki ga sabuwar gwamnati

Ministar kudi da tsare- tsaren kasar Zainab Shamsuna Ahmed ce Gwamnatin Najeriya na kammala cire tallafin man fetur kafin mika mulki ga sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayun wannan shekara, ta bayyana wannan kuduri a Abuja, inda ta ke cewa shirin cire tallafin shi ne wanda jama’a basa so amma kuma ya zama wajibi, a dai dai lokacin da akasarin ‘yan Najeriya suka yarda cewar tallafin baya taimakon talaka. 

Zainab Ahmed ta ce sun samu umurnin cire tallafin nan da watan Yuni na wannan shekara kamar yadda majalisa ta amince da shi a cikin kasafin kudin wannan shekara, kuma za su aiwatar da shi domin bai wa kasuwa damar samar da farashin a koda yaushe. 

Ministar ta ce idan an cire tallafin, zai ba iwa ‘yan kasuwa da masu zuba jari damar shiga harkokin kasuwancin man da kuma samar da shi ga al’umma. 

Zainab Ahmed ta ce, kawo karshen zuba tallafin man zai bai wa gwamnati damar karkata kudin da ake sanyawa zuwa bangarori da dama da suka hada da inganta asibitoci da makarantu da kuma samar da kayan more rayuwa. 

Asmau Uba Muhammad
485 0

Ra'ayoyi

Ajiye mana ra'ayinka

Wasikun Labarai

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Muhimmai

Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28
Majalisar dokokin Najeriy
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47
Gwamnatin tarayyar Najeri
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47
Gwamnatin Najeriya na kam
Wasanni / 2023-01-23 13:15:52
MAN UNITED ZA TA KARA DA
Wasanni / 2023-01-23 13:17:01
NAJERIYA TA CI FARANSA, G

Tambarin Hausa

Tambarin Hausa Tv, gidan Talabijin guda daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta da harshen Hausa

Quick Links

© Amasis Broadcasting Services LTD.. All Rights Reserved.