Tuesday 3rd gam October 2023
No record found
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dage Shirin kidaya da aka tsara gudanarwa a fadin kasar.

Ministan yada labarai da al’adu na kasar, Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dage Shirin kidaya da aka tsara gudanarwa a fadin kasar zuwa watan Mayun2023. ya bayyana hakan  ne jim kadan bayan fitowa daga taron majalisar zartarwar kasar wanda ya gudana karkashin jagoranci shugaba Muhammadu Buhari a ranar Larab a a birnin Abuja.

A cewar Lai Muhammad daukar wannan matakin ya zama wajibi sakamakon yadda hukumar zaben kasar ta dage zaben gwamnoni zuwa ranar asabar, 18 ga watan Maris da muke ciki. Yana mai cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta kuma ware naira biliyan 2 da miliyan dari 8 ga hukumar kidaya ta kasar domin ta mallaki na’u’rorin da za a yi amfani da su wajen kidayar ta bana.

Idan dai za a iya tunawa tun da fari gwamnati ta sanar da ranar 29 ga watan Maris din da  muke ciki a matsayin ranar da za a fara kidayar jama’a da gidaje a fadin Najeriyar, koda yake sauye-sauyen da aka samu masu jibi da al’amuran zabe ya tilasta sauya lokacin gudanar da kidayar.

 

Asmau Uba Muhammad
455 0

Ra'ayoyi

Ajiye mana ra'ayinka

Wasikun Labarai

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Muhimmai

Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28
Majalisar dokokin Najeriy
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47
Gwamnatin tarayyar Najeri
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47
Gwamnatin Najeriya na kam
Wasanni / 2023-01-23 13:15:52
MAN UNITED ZA TA KARA DA
Wasanni / 2023-01-23 13:17:01
NAJERIYA TA CI FARANSA, G

Tambarin Hausa

Tambarin Hausa Tv, gidan Talabijin guda daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta da harshen Hausa

Quick Links

© Amasis Broadcasting Services LTD.. All Rights Reserved.