Saturday 3rd of June 2023
No record found
Labaran Duniya / 2023-03-15 20:31:06

Sakataren Harkokin wajen Amirka , ya bukaci samar da mafita ga rikicin da ya daidaita kasar Habasha

Sakataren Harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya  gana da firaministan Habasha Abiy Ahmed, da nufin samar da mafita ga rikicin da ya daidaita kasar, har wa yau, jami’in zai yi amfani da wannan dama wajen cimma daidaito a huldar da ke tsakanin Amirka da Habasha da ta yi tsami a sakamakon rikicin kasar da ake zargin firaiminista Abiy Ahmed da aikata ba daidai ba.

Blinken shi ne babban jami in Amirka da ya ziyarci kasar da ta kasance ta biyu mafi yawan al’umma a Afirka baya ga Najeriya, tun bayan yakin da ya barke a karshen shekarar 2020 tsakanin rundunar gwamnatin Habasha da yan gwagwarmaya na yankin Tigray, matakin da firaiminista ya dauka a yakin ya janyo masa bakin jini da jerin takunkumai daga kasashen yamma musanman Amirka da yanzu ke kokarin dinke wannan barakar. 

 Rikicin kasar ta Habasha ya lakume daruruwan rayuka baya ga wasu kusan miliyan guda da suka rasa matsuguni.

 

Asmau Uba Muhammad
416 0

Ra'ayoyi

Ajiye mana ra'ayinka

Wasikun Labarai

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Muhimmai

Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28
Majalisar dokokin Najeriy
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47
Gwamnatin tarayyar Najeri
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47
Gwamnatin Najeriya na kam
Wasanni / 2023-01-23 13:15:52
MAN UNITED ZA TA KARA DA
Wasanni / 2023-01-23 13:17:01
NAJERIYA TA CI FARANSA, G

Tambarin Hausa

Tambarin Hausa Tv, gidan Talabijin guda daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta da harshen Hausa

Quick Links

© Amasis Broadcasting Services LTD.. All Rights Reserved.