Tuesday 3rd gam October 2023
No record found
Labaran Duniya / 2023-03-15 19:40:58

Hukumar dake kula da kafafen yada labarai NBC ,ta sanyawa wasu kafafen yada labarai 25 takunkumi .

Daraktan hukumar dake kula da kafafen yada labarai na kasa Balarabe Shehu Illele  ya bayyana sanyawa wasu kafafen yada labarai 25 takunkumi sakamakon karya dokokin hukumar (NBC) a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

Bayanin na  zuwa ne  a ranar Laraba ,yayin da yake zantawa da manema labarai, ya kara da cewa hukumar ta kuma baiwa wasu kafafen yada labarai 16 gargadi domin su gyara ayyukansu.

Ya kara da cewa wasu daga cikin wadannan kafafen yada labaran , sun baiwa baki da masu fashin baki har ma da masu kiran waya a yayin shirye-shirye damar furta wasu kalmomi mara sa da dadi ba tare da yi musu linzami ba.

Balarabe Illela ya kuma bukaci sauran kafafen yada labaran kasar da su mayar da hankali wajen sanya kwarewa da kuma bin doka da oda yayin gudanar da ayyukansu.

Asmau Uba Muhammad
311 0

Ra'ayoyi

Ajiye mana ra'ayinka

Wasikun Labarai

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Muhimmai

Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28
Majalisar dokokin Najeriy
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47
Gwamnatin tarayyar Najeri
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47
Gwamnatin Najeriya na kam
Wasanni / 2023-01-23 13:15:52
MAN UNITED ZA TA KARA DA
Wasanni / 2023-01-23 13:17:01
NAJERIYA TA CI FARANSA, G

Tambarin Hausa

Tambarin Hausa Tv, gidan Talabijin guda daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta da harshen Hausa

Quick Links

© Amasis Broadcasting Services LTD.. All Rights Reserved.