Saturday 3rd of June 2023
No record found
Labaran Duniya / 2023-03-09 12:22:58

Ziyarar Shugaban Kungiyar Ecowas a birnin Tunis

Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake kai hare-haren wariyar launin fata da ke shafar yan ci rani da ke kudu da hamadar Sahara a kasar da ke arewacin Afirka.

A lokacin da majalisar tsaron kasar ta gudanar da taro a watan da ya gabata, shugaba Kaies Saied ya danganta bakin haure da ba su da takardun izini da haifar da  tashin hankali da aikata laifuka.

Kungiyoyin kare hakkokin bil adama sun bayar da rahoton karuwar tashe tashen hankula da suka hada da kashe bakaken fata ‘yan Afirka, tun bayan kalaman da shugaban kasar ya yi na farko yayin da bakin haure ke cewa an jefar da su daga gidajensu baki daya aka mika su ga “adalcin ’yan sanda”.

A kwanakin baya ne aka dawo da dalibai da yan ciranin tattalin arziki daga kasashe, irin su Guinea da Mali da Ivory Coast da suka tsere daga Tunisia.

A farkon makon nan, hukumomin Tunisiya sun ba da sanarwar daukar matakin inganta yanayin yan kasashen waje a Tunisiya da kuma saukaka hanyoyin ga masu neman daidaita al amura a duk fadin kasar.


Asmau Uba Muhammad
417 0

Ra'ayoyi

Ajiye mana ra'ayinka

Wasikun Labarai

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Muhimmai

Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28
Majalisar dokokin Najeriy
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47
Gwamnatin tarayyar Najeri
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47
Gwamnatin Najeriya na kam
Wasanni / 2023-01-23 13:15:52
MAN UNITED ZA TA KARA DA
Wasanni / 2023-01-23 13:17:01
NAJERIYA TA CI FARANSA, G

Tambarin Hausa

Tambarin Hausa Tv, gidan Talabijin guda daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta da harshen Hausa

Quick Links

© Amasis Broadcasting Services LTD.. All Rights Reserved.