Saturday 3rd of June 2023
No record found
Labaran Duniya / 2023-02-13 13:10:25

SHUGABAN KASAR KAMARU NA BIKIN CIKA SHEKARU 90 DA HAIHUWA

Yau Litinin 13 ga watan Fanrairu 2023, ssugaban kasar Kamaru Paul Biya yake bikin cikarsa shekara 90 da haihuwa, kuma a matsayin shugaban kasar da ya fi dadewa a duniya a yanzu.

Shugaban ya taso ne a kauyen Mvomeka’a dake kudancin kasar a shekara ta 1933 kuma ya kama mulki a shekara ta 1982.

Wasu rahotanni na nuna cewa gazawar shugaban wajen inganta rayuwar ‘yan kasar da kuma tashe-tashen hankula dake samuwa daga ‘yan aware dake amfani da harshen turanci sun dusashe karsashin da gwamnatin shugaban ke da shi tun farko-farkon dalewarsa karagan mulki.

A yanzu dai ba a yawan ganin shugaban a bainar jama’a kuma yawanci ana ganin sa ne a kasashen waje.

A sakamakon dadewa da ‎ yan kasar suka yi basu ganshi ba a shekaru biyu da suka gabata har aka yada jita-jitar mutuwarsa a sanadiyar cutar korona.

Yan hamayya suna ta kira da ya sauka daga mulki, a yayinda kuma yan kusa dashi suke cewa ya ci gaba da mulki.

Ishaq Ahmad
456 1

Ra'ayoyi

Image
Test user 2018-11-21 12:25:56

This is sample text for testing.

Ajiye mana ra'ayinka

Wasikun Labarai

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Muhimmai

Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28
Majalisar dokokin Najeriy
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47
Gwamnatin tarayyar Najeri
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47
Gwamnatin Najeriya na kam
Wasanni / 2023-01-23 13:15:52
MAN UNITED ZA TA KARA DA
Wasanni / 2023-01-23 13:17:01
NAJERIYA TA CI FARANSA, G

Tambarin Hausa

Tambarin Hausa Tv, gidan Talabijin guda daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta da harshen Hausa

Quick Links

© Amasis Broadcasting Services LTD.. All Rights Reserved.