Tuesday 3rd gam October 2023
No record found
Siyasa / 2023-02-07 15:56:53

Matacce ya Lashe Zabe a ƙasar Ecuador

Ɗan takarar magajin gari a ƙasar Ecuador, wanda aka kashe sa o i gabanin fara kaɗa ƙuri a a zaɓen, ya yi nasarar lashe zaɓen magajin garin birnin Puerto López.

Wasu yan bindiga ne suka harbe Omar Menéndez mai shekaru 41, a ranar Asabar bayan da suka kutsa ɗakin da yake ganawa da jami an yaƙin neman zaɓensa, kuma wani matashi ma ya rasa ransa a lokacin harin. 

Kawo yanzu dai Yan sanda na ci gaba da bincike domin gano waɗanda ke da hannu a harin. Sai dai da wannan sakamakon zaben da ya fito a yanzu ake sa ran wani mamba a jam iyyarsu ya maye gurbinsa a matsayin magajin garin.

An gudanar da zaɓen ne a lokacin da ake ci gaba da ƙaruwar rikice-rikice masu alaƙa da yan shaye-shaye a ƙasar.

Ba mista Menéndez ne kaɗai ɗan siyasar da aka kashe gabanin zaɓen ba. Makonni biyu da suka gaba ma an harbe tare da kashe ɗan takarar magajin garin Salinas, Julio César Farachio.

Ishaq Ahmad
559 0

Ra'ayoyi

Ajiye mana ra'ayinka

Wasikun Labarai

Yi rajista domin kasancewa daya daga cikin masu samun labarai da dumi-duminsu daga babban Editanmu

Muhimmai

Gwamnati / 2023-01-25 13:57:28
Majalisar dokokin Najeriy
Gwamnati / 2023-03-15 21:11:47
Gwamnatin tarayyar Najeri
Gwamnati / 2023-03-15 21:27:47
Gwamnatin Najeriya na kam
Wasanni / 2023-01-23 13:15:52
MAN UNITED ZA TA KARA DA
Wasanni / 2023-01-23 13:17:01
NAJERIYA TA CI FARANSA, G

Tambarin Hausa

Tambarin Hausa Tv, gidan Talabijin guda daya tilo dake watsa shirye-shiryen ta da harshen Hausa

Quick Links

© Amasis Broadcasting Services LTD.. All Rights Reserved.