Na’urar bincike a duniyar Mars ta Sin ta aiko da sakon bidiyo da ta dauki kan ta

Tauraron dan adam na Tianwen-1 mallakar kasar Sin, ya aiko da hotunan bidiyo daga duniyar Mars, sakon dake kunshe da taya murnar zuwan sabuwar shekarar gargajiya ta kalandar kasar Sin.

Na’urar dake jikin tauraron, ta aiko da hotunan bidiyo da ta dauki kan ta a Litinin din nan, wato jajiberin sabuwar shekarar ta kasar Sin.

Hukumar dake lura da ayyukan samajannati ta Sin ko CNSA a takaice, ta fitar da bidiyon na’urar dake cikin kyakkyawan yanayi bisa falakin ta, cikin hotunan har da injin ta samfurin 3000N, da sashen tanki, da kuma injin sarrafa yanayin ayyukan ta.

Kaza lika bidiyon na dauke da hoton inuwar rana, dake sauka jikin tauraron. Ana kuma hango tutar kasar Sin, idan na’urar ta matsa saman sahen arewa na duniyar ta Mars. Tun da fari, an tsara na’urar ne don ta rika daukar hotuna na ayyukan sanya ido.

Ya zuwa Litinin din nan 31 ga watan Janairun 2022, tauraron Tianwen-1 ya yi aikin kewaya falakin sa har tsawon kwanaki 557, ya kuma yi tafiyar kilomita miliyan 3.5 daga doron duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.