Najeriya: Wasu ‘Yan Bindiga sun yi dirar-mikiya a gidan Shugaban Kungiyar Malaman Jami’a

Wasu ‘yan bindiga sun yi dirar-mikiya a gidan shugaban kungiyar malaman jami’a ta Tarayya Najeriya reshen Jihar Zamfara, da ke Gusau a arewa maso gabashin kasar.

An bayyana cewa ‘yan bindigar sun mamaye gidan malamin ne wanda ke wajen garin inda suka bude wuta da harbin kan mai-uwa-da-wabi, maharan sun tafi da mutane biyar a gidan, wadanda suka hada da wani dan dan-uwansa da ‘yar dan-uwansa da kaninsa da kuma kannen matarsa mata.

Bayan wadannan ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wani makwabcin gidan, wanda ma’aikacin jami’ar ne shi ma, mai suna Alhaji Abbas.

Daman masu satar mutane sun sha kai hari a baya a wannan unguwa ta Damba, wannan shi ne karo na uku da aka kai hari inda ake sace mutane a rukunin gidajen.

Leave a Reply

Your email address will not be published.