Najeriya: NAPTIP Tayi nasarar ceto mutane 61 da akayi yunkurin tsallakawa dasu kasar Libya

Hukumar yaki da bautarwa da fataucin bil adama a Najeriya wato NAPTIP tayi nasarar ceto wasu mata da maza ‘yan kasar ta najeriya 61 da aka yi yunƙurin safarar su zuwa kasar Libya ta Jamhuriyar Nijar.

Hukumar ta NAPTIP ta sami nasarar ceto mutanen ne bayan da jami’an ’yan sandan Jamhuriyar Nijar, suka kamo su a lokacin da duke sintirin iyaka a cikin wani daji a kasar ta Nijar.

Cikin adadin mutanen da aka ceto shekarun su sun kama ne daga 17 zuwa 50, sannan 29 daga cikinsu maza ne.

Daya daga cikin mazan 29 da hukumar yaki da bautarwa da fataucin dan Adam ta ceto wanda dan asalin Jihar Kano, ya bayyana yadda tafiyar tasu ta kasance, inda ya ce sun sha matuƙar wahala kuma sun yi da nasanin tafiyar.

Sakamakon ƙaruwar fataucin bil adama a Tarayyar Najeriya tuni hukumar ta NAPTIP ta kafa wasu kwamitoci na kar ta kwana a wasu jihohin kasar ciki har da Kano da Jigawa da Kaduna da kuma Katsina don shigar da al’umma cikin yaki da fataucin dan Adam da cin zarafin al’umma da ke kara hauhawa a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.