Najeriya: Mutane shida ne suka rasa rayukan su a sakamakon wasu hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a jihar Neja

Akalla mutane shida ne suka rasa rayukan su a sakamakon wasu hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a jihar Nejan dake Arewacin Najeriya.

Hare-haren da ‘yan fashin dajin suka kai a karamar hukumar Mariga yayi sanadiyyar jikkata wasu mutane da dama da kuma yin garkuwa da wasu da dama.

wani tsohon dan majalisar dokokin Jihar Nejan dan asalin yankin Hon. Usman Musa ya shaidawa manema labarai cewa maharan sun balle  shagunan mutane da kuma kona gidajen jama’a a garuruwan Gulbin Boka da Ragada da kuma garin kasuwar Garba.

Sai dai duk kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Nejan yaci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published.