Najeriya: INEC ta bayyana Shirin ta na gudanar da sahihin zabe.

Hukumar zabe ta Najeriya wato INEC ta bayyana Shirin ta na gudanar da sahihin zabe da samar da tsaro a lokacin zaben kananan hukumomin a birnin Abuja da za’a gudanar a ranar asabar 12 ga watan da muke ciki.

Shugaban hukumar zaben Prof Mahmud Yakubu da kuma babban sufeton ‘yan sanda na kasar Alkali Baba Usman suka bada da tabbacin hakan lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar talata a birnin Abuja.

Hukumar ta kuma ja hankalin mazauna da sauran masu ruwa da tsaki da suyi watsi da duk wani abu daka iya tayar da rkici a yayin zaben.

A nasa bangaren, babban sufeton ‘yan sanda  Alkali Baba Usman, wanda ya samu wakilcin DCP Basil Idegwu ya bada tabbacin samar da jami’an tsaro domin ganin an gudanar da zaben lami lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.