Najeriya: Hukumar Kwastam ta kama hodar ibilis da kudin ta ya kai kimanin naira biliyan 4 a iyakar Seme

Hukumar Kwastam a Najeriya ta sanar da kama  hodar ibilis (cocaine) da kudin sa ya kai naira kusan biliyan 4 akan iyakar Seme dake Badagry.

Kwamandan kwastam dake kula da iyakar Bello Muhammad Jibo ya sanar da wannan gagarumar nasarar da suka samu, lokacin da yake gabatar da hodar tare da wasu kayayyakin da jami’an sa suka kama.

Jami’an Kwastam na ci gaba da dakile yunkurin bata gari wajen shigar da kwayoyi kasar ta kan iyaka.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.