Najeriya: Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya haramta zirga-zirgar Babura a Jihar Adamawa

Gwamnan jihar Adamawa da ke Arewacin Najeriya Ahmadu Umaru Fintiri ya haramta zirga-zirgar Babura a wasu yankunan jihar daga karfe 5 na Asuba zuwa 5 na yammaci.

Umarnin na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Umwashi Wonosikou ya fitar a ranar Talata, inda umarnin zai fara aiki tun daga ranar 8 ga watan da mu ke ciki har sai abinda hali yayi.

Sanarwar ta kara da cewa matakin haramcin ya biyo bayan karuwar ayyukan bata gari da ke zama barazana ga zaman lafiyar jihar.

Dokardai ta shafiwasuyankuna a kanananhukumominGirei da Yola ta kudu

haka kuma umarnin ya samar da hukuncin daurin watanni 6 a gidan gyaran hali ko zabin tarar Naira dubu 100 ko hada biyun du ka ga masu Baburan da aka kama da karya dokar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.