Najeriya: Dibu Ojerinde, ya nemi alfarmar a shari’ar da ake yi da shi

Tsohon shugaban hukumar JAMB ta Najeriya, Dibu Ojerinde, ya nemi alfarmar a shari’ar da ake yi da shi a babban kotun tarayya a Abuja.

A ranar Talata ne lauya mai kare Dibu Ojerinde, Ibrahim Ishyaku ya bayyana haka, inda  Ishyaku ya sanar da Alkali cewa za su tattauna a kan yadda za a warware matsalar a wajen kotu.

Haka kuma, Ibrahim Ishyaku ya roki mai shari’a Obiora Egwuatu ya ba su kwana daya domin su zauna da hukumar ICPC da ke tuhumar wanda ake kara. Yana mai bukatar cigaba da shari’ar nan da sa’o’i 24 idan har an gaza samun matsaya tsakanin wanda yake karewa da ICPC.

Lauyan da ya shigar da kara a madadin hukumar ICPC, Ebenezer Sogunle, bai nuna adawarsa ga wannan bukata da takwaran na sa ya bijiro da shi ba, inda ya bukaci ayi zama a ranar Laraba, 9 ga watan Fubrairu 2022 domin a saurari shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.