NAJERIYA: Dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Ibrahim Na-idda, YA RASU

Wani dan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltan mazabar Gusau 1, Ibrahim Na-Idda, ya rigamu gidan gaskiya. Dan majalisar ya mutu ne da daren Juma’a a Asibiti FMC Gusau bayan doguwar rashin lafiya da yayi, Dan majalisar ya mutu yana mai shekaru Sittin da bakwai (67)

Dirakta Janar na yada labarai da hulda da jama’a na majalisar dokokin, Jafaru Kaura, ya bayyana hakan. Tuni an yi jana’izarsa bisa koyarwan addinin Musulunci.

Marigayi Ibrahim Na-Idda ya bar mata hudu, ‘yaya ashirin da shida da sauran yan’uwa. Mutuwar Na-Idda na zuwa ne watanni shida bayan mutuwar Hon. Ibrahim Ahmad da ya wakilci mazabar Shinkafi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.