Mutane Milyan 91 na cikin bakin talauci a Najeriya.

Kungiyar tattalin arzikin Najeriya, NESG, ta bayyana cewa yan Najeriya milyan 91 ke cikin bakin talauci yanzu haka a fadin tarayya. Shugaban kungiyar, Mr. Asue Ighodalo, ya bayyana hakan ranar Talata, a taron kaddamar da takardar hasashen tattalin arzikin 2022, a Abuja.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen inganta rayukan jama’arta a shekarar 2022 maimakon mayar da hankali kan lamuran siyasa. A cewar shugaban kungiyar, idan gwamnati ta bari siyasa ya dauke mata hankali, za’a yi asarar yan nasarorin da aka samu.

Mr. Asue Ighodalo, ya yi kira ga yan Najeriya su zabi mutumin kirki wanda aka tabbatar zai iya inganta tattalin arzikin kasar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.