Mali tafara Alhini na kwanaki 3 Don Jimamin Harin da Yayi sanadiyyar Mutuwar Sojoji 42

Gwamnatin Sojin Mali ta ayyana makokin kwanaki 3 bayan kisan Sojojinta 42 a harin ta’addancin lahadin makon jiya a garin Tessit na yankin Gao a arewacin kasar.

Sanarwar da fadar gwamnati ta fitar ta ce ‘yan ta’addan sun yi amfani salon yaudara ta hanyar dana bom a jikin wasu manyan motoci wanda ya kashe tarin Sojojin.

A cewar sanarwar ‘yan ta’adda sun yi amfani da makaman roka da na atilare da kuma jirage marasa matuka wajen kaddamar da farmakin.

Sanarwar wadda kakakin gwamnati Ibrahim Traore ya karanto kai tsaye ta gidan talabijin din kasar ya ce Mali ta yi rashin Sojojinta 42 a gumurzun da ya barke bayan kwanton baunar na ‘yan ta’addan.

Traore ya ci gaba da cewa a gwabzawar da aka shafe lokaci ana yi, Sojin na Mali sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 37 tare da lalata manyan makaman da suka kai farmakin da su.

Bayan harin wanda kungiyar JNIM mai biyayya ga Al-Qaida ta dauki alhaki wani makamancin farmakin ya kuma kashe wasu jami’an ‘yan sanda

Leave a Reply

Your email address will not be published.