Kenyatta ya bada tabbacin mika mulki cikin ruwan sanyi

Karo na farko tun bayan sanar da sakamakon zaben Kenya, shugaba Uhuru Kenyatta ya ba da tabbacin mika mulki cikin kwanciyar hankali ga wanda ya yi nasarar lashe zaben da aka yi a ranar 9 ga wannan watan.

Shugaban mai barin gado ya ba da wannan tabbaci ne a yayin wata ganawar da wakilan addinai inda da ya ke cewa babu shakka zai mika mulkin cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.

Har yanzu dai bai fito fili ya taya mataimakin sa William Ruto wanda ya lashe zaben da kuri’u kusan 233,000 murna ba.

Ruto wanda bai samu goyon bayan Kenyatta ba, ya yi nasarar lashe zaben na Kenya ne bayan nasara kan Raila Odinga madugun adawar kasar da ya samu goyon bayan shugaba Uhuru Kenyatta a zaben na watan nan.

A zabukan baya da suka gudana dai an sha fuskantar matsalar rikici bayan zabe wanda ke juyewa zuwa na kabilanci da kuma haddasa asarar dimbin rayuka dalilin da ya sanya fargaba a wannan karon, musamman bayan da Odinga ya yi watsi da sakamakon zabe.

Leave a Reply

Your email address will not be published.