Kasashe 143 sun kada kuri’ar yin tir da Allah wadai da mamayar Rasha a Ukraine

Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’ar yin tir da Rasha kan mamaye wasu sassan Ukraine da ta yi, matakin da shugaban Amurka Joe Biden ya ce sako ne mai karfi ga takwaransa Vladmir Putin.

Kasashe 143 ne suka goyi bayan kudurin na yin tir da Rasha a zauren Majalisar Dinkin Duniyar, inda 5 suka hau kujerar naki, sauran kasashe 35 kuma suka kauracewa zaman, wadanda suka hada da China, India, Afirka ta Kudu da kuma Pakistan, duk da matsin lambar da Amurka ta rika musu kan su yi tir da Rashan.

Kudurin dai ya yi tir da matakin Rasha, na shirya  zaben raba gardama a cikin iyakokin Ukraine” da kuma “yunkurin mamaye yankuna hudu na kasar ta karfin tsiya da shugaba Vladimir Putin ya sanar a watan jiya.

Ko a watan Satumban da ya gabata, sai da Majalisar ta nufaci kada makamanciyar kuri’ar amma Rasha ta yi amfani da kujerarta wajen dakile yunkurin duk da matakin Amurka na kafiya don tabbatar da ganin an yi tir da Moscow.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *