Kamaru ta nisanta kanta da yin coge a gwajin Korona ga yan kwallonta.

Kasar kamaru dake daukar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afrika CAN ta 2022 da tun farkon kafin soma gasar ta bayyana gano yan wasanta 4 da suka kamu da annobar covid 19 har zuwa yau bata sake bayyana bulluwar annobar ba.

Wani al’amari da ya haifar da alamun tambaya da mamaki  daga sauran tawagogin da suka halarci gasar, to sai dai a tattaunawarsa da RFI, Samuel Eto’o, shugaban hukumar kwallon kafar kasar ta Kamaru ya bayyana takaicinsa kan zargi da yan gunagunin da ake yi wa kasar.

A lokacin wannan gasar ta cin kofin kwallon kafar nahiyar Afrika   CAN 2022, kasar Kameru, da ya kamata ta shirya gasar a 2019 bayan dauke ta  daga kasar Masar na fuskantar barazana daga makiyaya annobar Covid-19  da nau’in Omicron.

Kunkiyoyin kwallon kafar kasashe da dama ne dai suka shiga rudu sakamakon bullar annobar ta covid 19 a cikin su, da suka hada da Sénégal, Tunisie, Burkina Faso, Zimbabwe, Cap-Vert ko kuma Gabon da aka raba da tauraronta  (Pierre-Emerick Aubameyang). tun farkon soma gasar, haka kuma annobar ta shafi  kungiyar kwallon kasar Tunisiya. kafin buga wasanta na rukuni da kasar  la Gambie, inda gwaji ya tabbatar da yan kwallonta 12 dauke da  kwayar cutar ta covid 19.

Ita mai dai kasar komoros, ta buga wasanta na yan 8 da kasar Kamaru ba tare da mai tsaron gidanta ba, to sai dai abin mamaki mai masaukin bakin kasar Kamaru sumul kakal ta tsira daga annobar abinda ya haifar da yan gunagunin da mamaki daga wasu abokan hamayarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.