KAI-TSAYE Shirin Gyaran Tsarin Mulkin Najeriya Na 5 Ya Gamu Da Cikas A Yada Shirin Gyaran Tsarin Mulkin Najeriya Na 5 Ya Gamu Da Cikas

Kwamitin Majalisar Dokokin Najeriya kan gyaran  gyara Kundin tsarin Mulkin kasar na shekarar  1999, ya zargi gwamnonin jihohi 25 da yin katsalandan tare da kawo tsaiko ga shirin samar da sabon kundin tsarin mulki a kasar.

Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da   gyare -gyare 44 wadanda kwamitin ya kammala aiki akan su, har ya aika da su Majalisun Jihohin kasar 36 domin su amince da su, sai dai hakan ya ci tira.

Shugaban Kwamitin wanda shi ne mataimakin shugaban Majalisar Dattawa Ovie Omo Agege ya ce maimakon kwamitin ya samu takardar amincewar jihohin sai aka aiko masu da wata takarda mai dauke da wata bukata ta daban daga Majalisun Jihohi 25.`

Omo Agege ya ce Majalisun jihohin sun ce kafin su amince da wadannan kudurori 44 da kwamitin ya mika masu, sai an ba jihohin izinin zartar da kudurin dokar ‘yan sandan jiha, sannan a ba Majalisun jihohi damar cin gashin kansu da kuma wasu bukatu guda biyu.

Omo Agege ya kara da cewa, a ganin sa gwamnonin Jihohin na katsalandan musamman wajen adawa da kudurorin bayar da ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi, kuma wannan shi ne abinda ba sa so su gani domin suna amfana da asusun hadin gwiwa da ake yi tsakanin gwamnatocin jihohi da kananan hukumomin.

Shi ma mataimakin mai tsawatarwa a Majalisar Dattawa kuma daya cikin ‘ya’yan kwamitin Aliyu Sabi Abdullahi ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su yi tuhuma mai tsanani ga majalisun jihohin, domin kin amincewa da kudurorin tamkar rashin mutunta tsarin mulkin kasar ne.

A lokacin da yake nazari akan batun, Sanata Yusuf Abubakar Yusuf ya nuna cewa, idan majalisun jihohin ba su mutunta aikin Majalisar Dokoki ba, to akwai matsala

Kwamitin ya aika da kudurori 44 zuwa majalisun jihohi 36 a ranar 29 ga watan Maris na wannan shekara ta 2022 don neman amincewar su, kamar yadda sashe na 9 karamin sashi na 2 na Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya tanada, amma Jihohi 11 ne kadai suka amince da kudurorin, da suka hada da Jihar Lagos, Abia, Akwa Ibom, Anambra, Delta da Jihar Edo, sauran sun hada da Katsina, Kaduna, Ogun da jihar Osun.

Saurari cikakken rahoton daga Medina Dauda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *