JAMUS: Rasha za ta yaba wa aya zaki idan ta mamaye Ukraine

Jamus ta lashi takobin cewa muddin Rasha ta mamaye Ukraine za ta yabawa aya zaki, domin za’a antaya mata jerin takunkumai har da sukurkuta yarjejeniyar aikin samar da bututun gas zuwa Turai.

Ministar harkokin waje na Jamus Annalena Baerbock ta shaida wa  majalisar kasar tasu haka, inda ta ke cewa Jamus, tare da sauran kasashen Turai zasu malkaya wa Rasha takunkuman karairaya tattalin arziki wanda zai shafi aikin samar da bututun iskar gas da Rasha za ta tura wa kasashen yammaci da aka yi wa lakabi da Nord Stream 2.

A ‘yan shekarun da suka gabata, Kafewar da Jamus ta yi don samar da wannan bututun iskar gas daga Rasha, na kudaden da suka kai Euro Bilyan 10, kwatankwacin Dallar Amurka Biliyan 12, ya harzuka sauran kasashen yammaci ainun, inda suke ganin zai sa su rika dogaro da Rashar.

Shi wannan aikin samar da bututun iskar Gas, an tsarashi ne ta yadda zai samar da Gas da rahusa daga Rasha, zuwa Jamus, wadda ke sahun gaba wajen karfin tattalin arziki a Turai, a kokarin jingine mu’amulla da makamashin Coal da na Nukiliya.

A martanin Rashar, ta bakin Minstan tattalin arzikin kasar, idan har aka kirba masu takunkumi to kuwa ita ma Jamus za ta gane kurenta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.