Jam’iyyar NNPP ta yi Allah-wadai Da Yunkurin Ciwo bashin Naira biliyan 10 Domin Sanya kyamarorin CCTV a Jihar Kano

A sanarwar da shugaban Jam’iyyar ta NNPP na jihar Kano Hon. Umar Haruna Doguwa ya sanyawa hannu.

Jam’iyyar ta yi tir da bukatar Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na neman karbo rancen Naira biliyan 10 daga bankin Acess don sanya na’urorin daukar hoto na CCTV a jihar.

Jam’iyyar ta bayyana cewa, ba za ta iya zuba ido tana kallon gwamnatin ta Ganduje tana tarawa jihar Kano basussuka ba tare da yin abin da ya dace dasu ba.

A cewar jam’iyyar, Ga dukkan alamu Gwamna Ganduje yana amfani da kujerarsa wajen yin gaban kansa tare da jingine makomar jihar,
Sakamakon gaza biyan kudin jarrabawar kammala sakandire ga daliban jihar wanda hakan ya tilastawa dalibai da dama jingine ci gaba da karatu a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa bashin siyan kyamarorin yazo daidai da lokacin da gwamnatin ta Ganduje tayi watsi da magance matsananciyar matsalar rashin ruwa da taki ci ta ki cinyewa a fadin jihar,

jam’iyyar ta yi kira ga majalisar dokokin jihar da ta daina sahalewa gwamnatin ta Ganduje irin wadannan bukatun da basu da muhimmanci,

Amaimakon haka jam’iyyar ta yi kira ga ‘yan majalisar su sanya bukatun mutanen jihar Kano a gaba, tare da bijirewa burin gwamnan jihar, wanda jamiyyar ta bayyana a matsayin burin ruguza makomar jihar gabanin ta kwace mulki daga hannunsu a babban zaben 2023 mai zuwa.

Haka kuma jam’iyyar ta yi kira ga bankin Access da ya bijirewa duk wani yunkurin da zai baiwa Gwamnatin Ganduje damar cin bashi wanda ke kama da jinginar da jihar domin biyan bukatun kashin kai.

Jamiyyar ta kara da cewa ko a baya Gwanma Ganduje ya ciyo bashin Naira biliyan goma sha biyar kan gyaran ilimi, amma aka karkatar da kudin zuwa wani abu daban, wanda hakan ya kai ga dimbin dalibai sun daina zuwa makaranta saboda gwamnati ba za ta iya daukar nauyin jarabawarsu ba.

Jamiyyar ta NNPP ta yi zargin cewa, wannan kudi naira biliyan goma da majalisar dokokin jihar ta sahale a baya-bayan nan, na nufin biyan wasu makudan kudade da aka karkatar da su da gangan a lokacin zabukan fidda gwani na jam’iyya mai mulki.

A karshe jam’iyyar ta ja hankalin dukkan bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin bayar da lamuni na kudi a ciki da wajen Najeriya da su yi taka-tsan-tsan da bukatar Gwamna Ganduje na neman lamuni domin ko ta yaya gwamnati mai zuwa ba za ta mutunta irin wannan rancen na gaggauwa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.