Jami’an Binciken manyan Laifuka ta Amurica FBI Sun yi Dirar Mikiya Gidan Trump a Florida

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce jami’an hukumar binciken manyan laifuka ta FBI sun kai samame a gidansa na Mar-a-Lago da ke Palm Beach a jihar Florida.

“Kyakkyawan gidana, Mar-A-Lago da ke Palm Beach Florida a halin yanzu yana hannun gungun jami’an FBI,” in ji Trump a wata doguwar sanarwa da yammacin ranar Litinin. “Bayan bada hadin kai ga hukumomin gwamnati da abin ya shafa, wannan samame da aka kai gidana ba tare da sanarwa ba bai dace ba.”

Kafafen yada labarai sun ce ba a bayyana halin da ake ciki a binciken ba. Ma’aikatar Shari’a, duk da haka, tana ci gaba da bincike kan gano bayanan sirri a cikin akwatunan bayanan da aka kai gidan Trump a Florida bayan ya bar fadar White House a watan Janairun shekarar 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published.