Jamhuriyar Demokradiyyar Congo: wasu ‘Yan bindiga sun kai hari a sansanin mutanen da aka raba da matsugunin su dake gabashin kasar inda suka kashe akalla mutane 40.

Kungiyar dake sanya ido a Yankin Kivu tace ‘Yan bindigar sun kai harin da wukake ne daren jiya inda suka hallaka mutanen a Plaine Savo. Jami’an yankin da kungiyoyin fararen hula sun ce adadin wadanda aka kashe ya zarce 50, yayin da kakakin sojin yankin Ituri Laftanar Jules Ngongo yace sun tabbatar da mutuwar mutane 21 ne.

Kungiyar dake sanya ido akan rikicin yankin tace wata kungiyar ‘Yan bindiga da ake kira CODECO ce ta kai harin, wanda ta danganta shi da kisan kabilanci da ake fama da shi a wurin.

‘Yankin Djugu dake iyaka da Tafkin Albert da kuma kasar Uganda ya zama wani dandalin zubda jini na dogon lokaci tsakanin ‘Yan kabilar Lendu da Hema. Fada tsakanin wadannan al’ummomi ya barke ne tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003, inda ya lakume rayukan dubban mutane kafin dakarun kasashen Turai su shawo kan sa ta hanyar aikin samar da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.