Hukumomi a Lebanon sun kama wani mutum da ya yi ikirarin cewa shi annabi ne da Ubangiji ya aiko shi da sako zuwa ga al’umma.

Hukumomi a Lebanon sun kama wani mutum da ya yi ikirarin cewa shi annabi ne da Ubangiji ya aiko shi da sako zuwa ga al’umma.

Nashat Mounzer ya fito a wani bidiyo rike da wani sandar katako a hannunsa da wani zane-zanen fenti a goshinsa, inda yake cewa Ubangiji ya aiko shi zuwa ga mutane don ya isar musu da wani sako.

Haka kuma ya rika kalaman batanci ga wata kasa kawar Lebanon din wadda ake kyautata zaton Masar ce.

Ba dai kai ga gane ainahin mutumin da kuma kasarsa ba, kodayake akwai rahotannin da ke cewa Nashat makadi ne da ya taba aiki a wani gidan caca da ke kasar ta Lebanon.

Shugabannin addini a kasar sun yi kira ga hukuma da ta dauki mataki a kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.