Haryanzu anacigaba da Kirga Kuri’u a Kasar Kenya

Zuwa yanzu hukumar zaben Kenya ta tattara akalla kashi 90 na kuri’un da al’ummar Kenya su ka kada a zaben shugaban kasa na jiya Talata, zaben da ya gudana ba tare da tashin hankali ba duk da hasashen yiwuwar fuskantar rikicin, ko da ya ke ba a fito zaben kamar yadda ya kamata ba a wasu sassan kasar.

Duk da ya ke zai dauki kwanaki gabanin iya fitar da sakamakon zabe, amma bayanai na nuna yadda ake tafiya kan-kan-kan tsakanin manyan ‘yan takarar kasar biyu wato tsohon Firaminista Raila Odinga da kuma mataimakin shugaban kasa William Ruto .

A jawabin da ya gabatar cikin daren Talata, shugagabn hukumar zaben kasar, Wafula Chebukati ya yi kira ga al’ummar Kenya su kasance masu hakuri a yayin da hukumarsa ke aikin kirga kuri’u.

Da dama na zaman dar dar a yayinda su ke dakon sakamakon zaben, ganin cewa tun daga shekarar 2002 babu wani zaben da ba a samun takaddama a kan sakamako ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.