Gwamnatin Najeriya ta cire mukaddashin babban akantan kasar Mr. Chukwuyere N. Anamekwe inda aka maye gurbinsa da Mr. Okolieaboh Ezeoke Sylvis

Gwamnatin Najeriya ta cire mukaddashin babban akantan kasar Mr. Chukwuyere N. Anamekwe inda aka maye gurbinsa da Mr. Okolieaboh Ezeoke Sylvis, wanda tsohon darekta ne a tsarin asusun gwamnati na bai-daya, wato, TSA (Treasury Single Account).
Rahotanni na cewa an maye gurbin mai rikon mukamin na Akanta-Janar din ne saboda hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa, EFCC, na bincike a kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *