Gwamnatin Najeriya ta bukaci a bude jami’o’i

Gwamnatin Najeriya ta umarci duk shugabannin jami’o’in kasar da ke karkashin kulawarta su koma bakin aiki tare da kyale dalibai su koma karbar darussa.

Wannan umarnin na zuwa ne bayan wata bakwai da aka shafe malaman jami’o’in gwamnatin tarayya na yajin aiki.

Gwamnatin Najeriya ta kai karar kungiyar malaman ta ASUU, inda a makon jiya kotun ta umarci malaman da su janye yakin aikin, sai dai kungiyar malaman ta daukaka kara, matakin da ka iya tsawaita wannan takaddama.

Wannan umarnin na bude jami’o’i na kunshe cikin wata takarda da hukumar kula da jami’o’in Najeriya, NUC ta aika wa shugabannin jami’o’i mallakan gwamantin tarayyar Najeriya, wadda babban sakataren hukumar ta NUC ya sanya wa hannu.

BBC ta gano cewa, Ministan Kwadago Dakta Chris Nigige ne ya mika hukuncin kotun ma’aikata ta Najeriya kai-tsaye ga Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu.

Daga nan ne Ministan Ilimin ya umarci a aiwatar da wannan matakin na bude jami’o’in, ta hannun ma’aikatar da ke kula da jami’o’in Najeriya NUC – matakin da shi ne aka aiwatar da safiyar yau Litinin.

Akwai kwafen wasikar a hukumar ta NUC wadda ta umarci shugabannin jami’o’i da su tabbatar cewa malaman jami’a karkashin kungiyar ASUU sun koma koyar da dalibai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *